1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

'Yan gudun hijira na Sudan a Yuganda

April 11, 2024

‘Yan gudun hijra na Sudan da ke kasar Yuganda sun gudanar da sallar idi cikin yanayi na damuwa ba tare da ziyartar 'yan uwa da abokan arziki ba, kamar yadda suka saba kafin yakin na Sudan.

https://p.dw.com/p/4efBD
'Yan gudun hijira na Sudan
'Yan gudun hijira na SudanHoto: Mohammad Ghannam/MSF/REUTERS

Galibin ‘yan gudun hijrar na Sudan sun yi addu‘ar samun zaman lafiya a Sudan duk kuwa da bacin ran da suke fuskanta na gaza gudanar da shagulgular salla cikin kwanciyar hankali kamar yadda suka saba. Sumayya Musa na daga cikin ‘yan gudun hijra da suka kauracewa yakin Sudan, ta ce ta kasa gudanar da bikin sallah saboda yawan tunanin tashin hankalin da ta gani kan hanyarta ta ficewa daga Sudan.

Karin Bayani: Musulmin Sudan na kokawa da rashin buda baki a Azumi

'Yan gudun hijira na Sudan
'Yan gudun hijira na SudanHoto: LUIS TATO/AFP

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa adadin mutanen da yakin Sudan ya raba da muhallansu ya kai milyan 8.2, da galibinsu ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijra da ke ciki da wajen Sudan.

Kazalika, hukumar tallafa wa kananan yara ta Save the Children ta yi gargadin cewa yara kimani dubu 230,000 da mata masu juna biyu da kuma wasu tarin matan masu shayarwa ka iya rasa rayukansu a ‘yan watanni masu zuwa sakamakon yunwa, idan har ba a dauki matakin gaggawa ba.

Wani ‘dan gudun hijrar Sudan da ya tsere wa rikicin daga yankin Al Kamlin na jihar Aljazeera Muna Abdulmuniem ya ce sam rayuwar babu dadi a Yuganda, ga kuma sallar Idl Fitr da ta zo cikin kuncin rayuwa, inda yake tunanin yanayin da 'yan uwansa da ke Sudan ke ciki.

'Yan gudun hijira na Sudan
'Yan gudun hijira na SudanHoto: LUIS TATO/AFP

Shi ma da yake zantawa da DW wani ‘dan gudun hijrar Sudan din da ke Kampala Nasruddeen Mohammed, wanda kuma ya rasa matarsa da ‘dansa daya a yakin na Sudan, ya ce yana hasashen cewa samun kyautatuwar lamarin, domin kawo karshen rikicin da ke faruwa. Kasar Yuganda ta karbi bakuncin ‘yan gudun hijrar sama da dubu 15,000 ciki kuwa har da masu neman mafaka tun bayan barkewar yakin Sudan a ranar 15 ga watan Afrilun 2023.