1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta ce babu wani abin fargaba kan fashewar bam a Isfahan

April 19, 2024

A daidai lokacin da ake cikin fargaba a kasar Iran sakamakon rahotannin karar tashin wani bam a yankin Isfahan, babban kwamandan sojojin kasar Siavosh Mihandoust ya ce babu wani abun da ya faru na zargin kai hari kasar.

https://p.dw.com/p/4ex3b
Wani gwajin makami mai linzami a yankin Isfahan a 2023
Wani gwajin makami mai linzami a yankin Isfahan a 2023Hoto: Iranian Army Office/ZUMA Wire/IMAGO Images

Kamfanin sufurin jiragen saman Dubai na Emirates ya sanar da dakatar da jigilar matafiya tsakanin Dubai da Tehran tare da karkatar da akalar jiragen kamfanin na bin sararin samaniyar Iran.

Karin bayani: Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare 300 da jirage marasa matuka

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da fadar White House ta fitar da sanarwar samun daftarin bukatar Isra'ila na kaiwa Iran hari, duk da cewa bata amince da bukatar hakan ba, acewar kafofin yada labaran Amurkan.

Karin bayani: Amurka ta ce babu yaki tsakaninta da Iran

Kazalika kasar Amurka ta sanar da al'ummarta da ke zaune a Isra'ila cewa dasu takaita zirga-zirga a fadin kasar tare da kebe