1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka ta ce babu yaki tsakaninta da Iran

April 15, 2024

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa Amurka ba za ta shiga martanin da Isra'ilan ke son mayarwa kan Iran ba, acewar majiyar fadar White House.

https://p.dw.com/p/4elJy
Mai magana da yawun fadar White House kan tsaron kasa, John Kirby
Mai magana da yawun fadar White House kan tsaron kasa, John KirbyHoto: Ken Cedeno/UPI/newscom/picture alliance

Kasar Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan kasar Isra'ila a ranar Asabar, a wani martani na ramuwar gayya kan harin da Isra'ilan ta kai ofishin karamin jakadancinta da ke kasar Siriya.

Karin bayani: Kasashen duniya sun caccaki Iran bayan harin Isra'ila 

Majiyar Amurkan ta kara da cewa Isra'ila tana da damar kare kanta daga duk wata barazana daga Siriya, kai harma da sauran kasashen duniya, wannan na daga cikin manufofin tsaron kasar, to amma Amurka ba za ta shiga cikin rikicin kai tsaye ba.

Karin bayani: Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare 300 da jirage marasa matuka

Mai magana da yawun fadar White House kan tsaron kasa, John Kirby, ya shaidawa kafar yada labaran ABC cewa Amurka za ta ci gaba da tallafawa Isra'ila domin ta kare kan ta amma ba ta son shiga yaki da Iran.