1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dakatar da saukar jiragen Rasha

June 2, 2021

Wata sabuwar takkadama ta kunno kai tsakanin kasashen Jamus da Rasha sakamakon kin bai wa jirgin saman Jamus na Lufthansa izinin sauka a Rashar.

https://p.dw.com/p/3uN3G
Russland Notlandung l Sukhoi Superjet-100 - Symbolbild
Hoto: picture alliance/dpa/TASS/S. Bobylev

Jamus ta dakatar da saukar irangen Rasha a cikin kasarta, a wani mataki na ramuwar gayya in ji wata sanarwa da ma'aikatar sufurin kasar ta fitar.

Matakin dai na zuwa ne bayan da kamfanin jiragen samar kasar ta Jamus na Lufthansa ya soke tashi zuwa kasar, sakamakon rashin samun izini daga Rashar.

Sai dai kawo yanzu ma'aikatar sufuri da ofishin jakadancin Jamus na cigaba da tattaunawa da hukumar sufurin jiragen sama ta Rasha domin lalubo bakin zaren. Kimanin jirage bakwai ne abin ya shafa daga ranar Talata wannan Larabar.