1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Kare hakkin dan Adam lokacin mulkin mallaka

April 10, 2024

An kawo Quane Martin Dibobe Jamus domin ya daɗa ƙara wa Jamusawa ƙaimi. Amma sai ya zama ɗan rajin kare haƙƙin dan Adam na farko da ya ƙalunalanci dangantaka da ke tsakanin Jamus da gundumomin da take yin mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/4ed0A
Mulkin Mallaka na Jamus a nahiyar Afirka
Mulkin Mallaka na Jamus a nahiyar AfirkaHoto: Comic Republic

Wane ne Quane Martin Dibobe?

An haifi Dibobe a kusa da garin Douala na Kamaru, a 1876, kuma mahaifinsa ya riƙe ƙaramin muƙami irin na siyasa. Ya yi karatu a makarantar mishan a Kamaru, inda ya koyi karatu da rubutu cikin harshen Jamusanci. Ya zo Jamus a cikin tsakiyar 1890 domin shiga babban bikin nune-nunen kayan tarihi na masana'antu a Berlin.

Wane biki ne na nune-nunen kayan tarihin mulkin mallakar da Jamus ta yi na farko a 1896?

An shirya wannan baje-koli ne da nufin nuna wa mutane cewa Jamus kasa ce mai bayar da dimbin damammaki. Sannan kuma akwai wani shirin farfaganda da ke tafe domin shawo kan Jamusawa su yarda cewa ya halatta Jamus ta mallaki gundumomin mulkin mallaka. Daga cikin abubuwan da ake nunawa akwai bayanai da hotuna da ke nuna rayuwa ta yau da kullum a gundumomin mulkin mallaka. A yau, mukan kira irin wannan nune-nune da gidan nune-nunen bil Adama.

Dibobe na ɗaya daga cikin sama da ‘yan Afirka guda 100 da suka sauka a Berlin wasu daga cikinsu an kai su ne da ƙarfin tsiya, waɗansu kuma yaudararsu aka yi da alƙawarin za a biya su. Sun zo ne daga gundumomin da Jamus ta yi wa mulkin mallaka na Namibiya da Togo da Tanzaniya da kuma Kamaru, an tattaro ƙabilun Herero da Nama da Masai, don a yi nune-nunen da su. Shi Dibobe an san shi ne da sunan lamba 76. A zahiri, shi da sauran ‘yan uwansa ba su yi kama da gidadawan ‘yan ƙasa da ake nuna su a ƙauyukan da aka ƙirƙira na jabu ba.

Kusan Jamusawa miliyan bakwai ne suka dinga yin tururuwa zuwa wajen bikin nune-nunen na tsawon watanni 6, domin su gan shi da sauran ‘yan uwansa, yayin da aka tursasa su suna kwatanta rayuwa irin ta girki da rawa da farauta a ƙauyukan da aka ƙirƙira na Afirka na bogi.

Birnin Berlin na Jamus
Birnin Berlin na JamusHoto: Tobias Schwarz/AFP

An tursasa Dibobe da sauran wasu mutane masu yawa, wajen yin gwaje-gwajen lafiya na cin mutunci, wanda ɗaliban kimiyyar wariyar launin fata marasa ƙwarewa na Jamus suke yi da niyyar tabbatar da ingancin ilimin kimiyyar nan na samun kyakkyawan iri na halittar ɗan Adam, wanda ilimin kimiyya ne da aka musanta shi.

Me Dibobe ya yi bayan bikin nune-nunen kayan tarihin?

Dibobe ya yi zamansa a Berlin, wanda da ma ba sabon abu ba ne. ‘Yan Afirka ƙalilan sukan samu karɓuwa a biranen Jamus, kuma suna iya samun ayyuka ko wuraren koyon ayyukan yi. Da farko sai da Dibobe ya fara zama mai sana'ar hannu kafin ya kama aiki da jirgin ƙasa na Berlin. Ya auri ‘yar mai gidan da yake haya, bayan da ƙungiyar mishan ɗin da ta yi wa Dibobe baftisma a Kamaru ta bayar da shaidar ta san shi.

Daga wajen 1902, Dibobe ya zamo matuƙin jirgin ƙasa na ƙarƙashin ƙasa na birnin Berlin wanda aiki ne mai daraja a wancan lokacin daga nan kuma sai ya zamo mai farin jini.

Ga abin da ya taɓa rubutawa: "Ta hanyar jajircewa da kuma nuna hali nagari, sai na samu amincewar mutane.”

Ko Dibobe Ya Dawo Kamaru Kuwa?

A 1907, mahukuntan mulkin mallaka sun aika shi Kamaru don yin tuntuɓa a kan shimfiɗa titin jirgin ƙasa a can. Har zuwa yau ɗin nan, ire-iren ayyukan raya ƙasa da Jamus ta yi a Kamaru sunan nan, wasu masana tarihi ma har sukan yi begen zamanin mulkin Jamus, musamman idan aka kwatanta zaman mugunta da Faransa da Birtaniya suka yi bayan da a 1919 suka karɓi gundumomin da Jamus ta yi wa mulkin mallaka.

Duk da haka, Dibobe ya yi mamaki a kan irin duka da ƙwacen kadarori da nuna wariyar launin fata da kuma musgunawar da ‘yan Kamaru suka sha a hannun kamfanonin Jamus.

Yaya matsayin waɗanda Jamus ta yi wa mulkin mallaka ya kasance?

Bayan da Dibobe ya dawo Jamus, ya shiga cikin yajin aikin ma'aikata, ya mara wa Jam'iyyar ‘yan gurguzu baya, kuma ya taka rawa sosai a ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama da aka kafa a 1914.

Bayan da baƙaƙen fata masu yawa suka sauka a birane kamar su Berlin da Hamburg da Bremen, Dibobe da sauran ‘yan uwansa da suka ci gaba da zama a Jamus, sun samu kansu a matsayin ‘yan ƙasar da ba su da ƙasa.

Sai dai kuma hukumomi ba su da niyyar ba wa talakawan da suka yi wa mulkin mallaka ‘yanci irin wanda suke ba wa ‘yan ƙasar Jamus, domin kuwa hakan na nufi sai doka ta yi aiki a kan kowa daidai da kowa da ke gundumomin da take yi wa mulkin mallaka.

Don haka a tsakiya 1919, sai Dibobe da sauran Jamusawa ‘yan asalin Afirka su 17, a madadin ‘yan Afirka da ke zaune a gundumomin da Jamus ta yi wa mulkin mallaka, suka kai ƙorafinsu ga gwamnati don samun wakilci da kuma daidaiton haƙƙi da kuma kawo ƙarshen aikin ƙadagon tilas, waɗanda suna daga cikin hujjoji har guda 32 da suka bayar, bayan kuma sun yi mubaya'a ga Jamhuriyar Weimar ta Jamus.

Mene ne sakamakon korafin da Dibobe ya rubuta?

A sakamakon Jamus ta sallama gundumominta na mulkin mallaka ga sauran ƙasashen Turai a bisa Yarjejeniyar kasa da kasa ta Versailles da aka ƙulla, don haka ba a samu biyan buƙatun ƙorafe-ƙorafen da aka yi ba.

Dibobe ya rasa aikinsa na tuƙin jirgin ƙasa. Ya yi ƙoƙarin komawa Kamaru a 1922. Amma kuma sai sababbin shugabannin mulkin mallaka na gundumar Faransa suka hana shi shiga ƙasar saboda suna tunanin zai iya jawo tashin hankali. A maimakon haka, sai Dibobe, wanda a lokacin yana ɗan shekaru 45, ya nufi Laberiya kuma daga nan ba a sake jin ɗuriyarsa ba. Ana zaton a can ya mutu. 

A sakamakon haka, ba a san Dibobe ba sosai a Kamaru, saboda a Jamus aka fi sanin tarihin abubuwan da ya yi.

Amma kuma bayan sama da shekaru 100, ana ɗaukar wannan ƙorafi da ya rubuta a matsayin ɗaya daga cikin muhimman takardu na siyasa a kan ‘yan gudun hijirar Afirka a farkon ƙarni na 21.

Gidan rediyon DW, da yake yaɗa shirye-shirye a duniya ne ya kawo muku shirin waiwaye a kan mulkin mallakar Jamus, tare da tallafin Ofishin harkokin kasashen waje na ƙasar Jamus. Waɗanda suka ba da shawarwari su ne Lily Mafela da Kwame Osei Kwarteng da kuma Reginald Kirey.