1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karancin man fetur na kara tsanani

Uwais Abubakar Idris
April 30, 2024

Matsalar karancin man fetur a Najeriya na kara tsanani musamman a manyan biranen kasar a dai dai lokacin da kungiyar dillalan man da kamfanin NNPC ke ci gaba da fitar da bayanai da ke sabawa juna a kan matsalar

https://p.dw.com/p/4fN7v
Wani gidan mai a Abuja
Wani gidan mai a AbujaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

An  dai dauki matakin nuna wa juna ‘yar yatsa a kan wannan matsala ta karancin man fetur din da ke kara yín kamari a kusan daukacin birane da kauyyukan Najeriya, inda matsalar ta jefa jama'a cikin mawuyacin halin. Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriyar ta bayyana cewa kodayake akwai karancin man amma dumbin bashin da suke bi na Naira bilyan 200 ya kara tazarar lamarin a cewar Alhaji Sirajo Kamba Yahya Kamba shugaban masu wuraren adana main a kungiyar ta Najeriya.

Karin Bayani: Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya

Cunkoson ababen hawa a gidan mai a Abuja, Najeriya
Cunkoson ababen hawa a gidan mai a Abuja, NajeriyaHoto: picture-alliance/AA/Stringer

Wakilin mu Uwais Abubakar Idris ya zaga zagaya wasu sassan Abuja inda ya tarar da dogayen layukan motoci a gidajen mai wanda ke nuna tsananta wahalar man fetur din. Tuni dai yan bumburutu suka sake bayyana saboda karancin man a Abuja bayan ban kwana da aka yi da sun a tsawon lokaci.

Karin Bayani: Karancin man fetur a Najeriya

Karancin man fetur a Kano, Najeriya
Karancin man fetur a Kano, NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Kamfanin man fetur na Najeriyar NNPC ya dage cewa akwai wadataccen mai domin 'yar matsala ce kawai aka samu kuma an shawo kanta. 

Karin Bayani: Najeriya: Fata kan matatar man Dangote

Najeriyar dai duk da wadatar man fetir da take da shi har yanzu ta kasa magance matsalar karancin man da ake fuskanta daga lokaci zuwa lokaci duk da janye tallafin da ta yi, da kuma ikirarin mika daukacin harakar ga hannun 'yan kasuwa.