1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Leverkusen na ci gaba da kare kambunta

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 29, 2024

Yayin da kungiyar kwallon kafa ta Leverkusen ke ci gaba da jan zarenta a saman tebur, makwabciyarta Borrussia Dortmund na kara barar da damarta ta zuwa wasannin Zakarun Turai.

https://p.dw.com/p/4fIW9
Hoto: Kirchner-Media/TH/picture alliance

Can a Ingila kuwa, har yanzu kokawar daukar kofin Premier League na ci gaba da zafi. Kungiyoyin kasashen Larabawa ciki har da Al Ahly da Esperance ta Tunissun  murkushe abokan karawarsu a wasannin kusa da na karshe na neman cin kofin zakarun Afirka da na confederation cup.

Madallah!  Espérance de Tunis da Al Ahly ta masar za su kara wasan karshe na neman lashe kofin zakarun Afirka a ranar 18 da 25 ga watan Mayun 2024. Wannan jadawalin ya samu ne  bayan da kungiyar ta Tunisiya ta yi wajen road da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu sakamakon doke da ci daya mai ban haushi a mataki na biyu na wasan kusa da na karshe.

African Football Champions League | ES Tunis -  Al Ahly (2023)
ES Tunis - Al Ahly Hoto: picture alliance / NurPhoto

Ita kuwa gagarabadau ta Masar wato Al Ahly mai rike da kambun gasar ta kori TP Mazembe na Kwango da ci 3-0 bayan suka yi kunnen doki a wasan farko. Wannan dai shi ne zai kasance wasan karshe na tara na Champons league din Afirka da Esperance za ta buga a tarihinta, amma kuma na farkocikin shekaru shidan da suka gabata, yayin da Al Ahly ta zama ja-gaba kasancewar ta lashe kofi 12 a tarihinta .

'Yan wasan Zamalek na Masar cikin sauki da arha sun doke takwarorinsu na Dreams FC na Ghana da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin CAF kuma suka tabbatar da cancantar zuwa wasan karshe. Ko da shi ke Zamalek ta taba lashe kambun zakaran kwallon kafar Afirka sau biyar a tarihinta, amma sau daya kawai ta taba lashe gasar cin kofin Confederation a 2019, saboda 'yan wasan na Alkahira sun cancanci zuwa wasan karshe na CAF a karo na biyu ke nan. 

CAF Champions League - Finale
Hoto: Sameh Abo Hassan/dpa/picture alliance

Sai dai a daya hannun, an soke karawa ta biyu tsakanin RS Berkane da USM Algers, kamar yadda ya gudana a makon da ya gabata, saboda haka wannan matsalar za ta iya zama vi gaba ga 'yan wasan Maroko na Berkane wadanda suka haye mataki na karshe ba tare da buga wasa ko da na minti daya ba. Idan za a iya tunawa dai, kwace rigunan 'yan wasan Berkane da hukumomin Aljaeriya suka yi a filin jirgin sama saboda suna dauke da taswirara yankin yammacin sahara ya kawo tseko a wasan da ya kamata a gudanar a makon da ya gabata. Yanzu dai tatabbata cewar RS Berkane ta Moroko za ta fuskanci Zamalek ta Masar a wasan karshe na cin kofin CAF a ranakun 12 da 19 ga Mayun 2024.

Kungiyar kwallon kafa ta Bayer 04 Leverkusen ta ci gaba da kare kambunta na wasanni ba tare da yin rashin nasara ba a kakar wasanni ta bana, bayan da ta tashi wasa canjaras biyu da biyu a fafatawarsu da Stuttgart a mako na 31. An dai kai mintuna na 96 Sturtgart din na da ci biyu Leverkusen na da ci daya, godiya ga dan wasan Leverkusen Robert Andrich wanda ya farke kwallo ta biyu ana daf da hura usir din karshe.

Fußball | Champions League 2012/13 Halbfinale  Borussia Dortmund vs Real Madrid
Hoto: John MacDougall/AFP/Getty Images

A yanzu dai Leverkusen ta buga wasanni 46 na Turai ba tare da rashin nasara ba, ciki har da wasanni 31 na Bundesliga. Ita kuwa Borussia Dortmund na shirin yin bankwana ne da gasar cin kofin zakarun Turai wato Champions League, bayan da ta gaza kai bantenta a gidan Leipzig da suke kan-kan-kan tare da kokawar neman gurbi na hudu a teburin Bundesliga na bana. Dortmund din dai ta kwashi kashinta a hannu da ci hudu da daya, duk da kwallo mai tsada da dan wasanta Jadon Sacho ya fara zira wa a rga ana mintuna 20 da take leda.

A sauran wasannin mako na 31 kuwa, Bochum ta karbi bakuncin Hoffenheim tare da lallasa ta da ci uku da biyu. Haka abin yake a filin wasa na Alianz Arena, inda Bayern Munich ta karbi bakuncin Frankfurt ta kuma caskara ta da ci buy da daya. Bremen kuwa ta bi Augsburg har gida ta yi mata duka kawo wuka da ci uku da nema, kana Wolfsburg ma ta bi Freiburg har gida ta lallasa ta da ci  biyu a daya. Wannan wasan ne ma sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye, kuma Mohamed Tidjani Hassane da Abdul-raheem Hassane suka kasance tare da da ku. Ga kadan daga cikin yadda wasan ya gudana.

Fußball Bundesliga 1. FSV Mainz 05 - 1. FC Köln | Torjubel
Hoto: Kai Pfaffenbach/REUTERS

An gai da Mohamed Tidjani Hassane da Abdul-raheem Hassane. Har yanzu dai ba ta sauya zani ba ga kungiyar kwallon kafa ta FC Cologne a barazanar tuntsurawa rukuni na biyu na Bundesliga, bayan da ta tashi kunnen doki daya da daya da takwararta ta Mainz. Borussia Mönchengladbach ta tashi babu ci a wasanta da Union Berlin, kana Heidenheim ta bi Darmstadt da tuni ta yanke kauna ta kuma caskara ta da ci daya mai ban haushi.

Shahararren dan wasan kwallon Tennis din nan Carlos Alcaraz ya bayyana cewa ya fara wasannin Madrid Open ba tare da jin ciwo a kafadarsa ba, biyo bayan ciwon da ya ji da ya hana a fara kkar wasannin ta bana tare da shi. Koda yake mai shekaru 20 a duniya, Alcaraz na fargaba kan iya kare kambunsa, sakamakon ciwon da ya jin. Ya dai yi kokarin kare kambun nasa a gasar Indian Open da aka fafata a watan Maris din da ya gabata tare da kai wa wasan kusa da na kusa da na karshe wato quarter-finals a Miami kafin ya gurde kafadar tasa, sai dai kuma ya gaza halartar wasannin Monte Carlo da Barcelona tare da dawowa fili a wanna gasa ta Madrid Open.

Großbritannien Harry und Meghan bei der Royal Wedding
Hoto: picture-alliance/Captital Pictures/S. Wood

A watan gobe ne ake sa ran Yarima Harry da uwar gidansa Meghan Markle za su ziyarci Najeriya, domin tattaunawa kan wasannin Invictus da Yariman na Ingila Harry ya samar a shekara ta 2014 da nufin taimakawa sojojin da suka jikkata da ma wadanda suke kwance babu lafiya. Wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin Najeriyar Birgediya Janaral Tukur Gusau ya fitar na nuni da cewa, Harry zai isa Afirka nahiyar da ya jima yana cewa tana damfare a ransa bayan ya halarci addu'o'in cika shekaru 10 da fara wasannin na Invictus a Mujami'ar St. Paul's Cathedral da ke birnin London. Najeriya na zaman guda daga cikin kasashen da suka halarci wasannin a bara, ksar da sojojinta ke yaki da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi tun shekara ta 2009.