1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darajar Naira za ta ja baya a 2024 - Bloomberg

Muhammad Bello
January 5, 2024

Kafar Bloomberg ta yi hasashen cewar darajar Naira ta Najeriya za ta samu koma baya a 2024 wanda ba a taba gani ba tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimukuradiyya a 1999

https://p.dw.com/p/4auii
Takardun kudin Naira Naira na Najeriya
Takardun kudin Naira Naira na NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

A cikin rahoton da ta fitar Bloomberg ta ce duk da yawan faduwa da darajar Naira ta yi a 2023, Nairar za ta sake fuskantar koma bayan daraja a 2024, irin koma bayan da ba a taba samu ba tun da kasar ta koma mulkin dimukuradiyya a 1999. Wannan koma baya da Nairar ta Najeriya ke fuskanta, ya sa ta zama ta uku a cikin kasashe 151, a lalacewar darajar kudade, bayan na Labanon da ke ta daya, da kuma Argentina mai matsayi na biyu.

Karin Bayani: Najeriya: Faduwar darajar Naira na kara kamari

Na'urar ATM a Lagos
Hoto: Olisa Chukwumah/DW

Bloomberg ta ce kudaden ajiya na Najeriya a kasashen waje, shi ma ya samu koma baya a cikin shekaru shidda da suka gabata. Koma bayan da Nairar ke samu, gami da janye tallafi kan farashin man fetur ya tsunduma jama'a cikin tsananin tsadar rayuwa.

Mr Ignatious Chukwu, mai sharhi ne kan tattalin arziki da kuma ke aiki da jaridar Business Day.

Ya ce darajar kudin ko wace kasa na dogara ne da bukatar da ke akwai na kudin, a hadahadar kasa da kasa, kuma hanyoyi biyu rak na dawo da darajar kudin da ya fadi, ta farko ita ce yin amfani da karfin mulki wajen hana shigowa da kayayyaki barkatai, ta biyu ita ce rairaye wasu kayayyaki da ko kadan ba a bukatar su a kasar, da kuma tabbatar da cewar ba a shigowa da su, ko da ya ke dai akwai 'yan fasa kwauri, akwai bukatar karfafa tsarin samar da kayayyakin bukata na cikin gida.

Takardun kudin Naira na Najeriya
Takardun kudin Naira na NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kan faduwar darajar da Nairar, Alhaji Balarabe Ikara dan canji a Fatakwal cewa ya yi.

Kwanan nan ne dai wasu alkaluma suka nuna cewar halin rayuwa ya sa 'yan Najeriya neman basuka a bankuna, da adadin ya kai Naira biliya 740 a shekarar 2024 kawai, domin kawai su iya ciyar da iyalansu.

Bemene Tanem, wani ne da ya bayyana yadda rayuwa ta dada taazzara a Najeriyar.

Ya ce masu ganin su ke da kasar sun kashe kasar, talakawa na ta wahala, tsadar rayuwa na dada taazzara, karancin albashin ma'aikata na 30,000 ba ya iya sayen buhun shinkafa, mafita kawai shi ne rantar kudade daga bankuna, wadda babu ma wannan damar a yanzu, ina ganin dai ana dosar yanayi na matukar damuwa