1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta kashe mutane 70 a Kenya

November 26, 2023

Gwamnatin kasar Kenya ta sha alwashin daukar matakan magance bala'in ambaliyar ruwa da ya yi sanadin mutuwar mutane 70 a kasar, tare da raba dubunnan mutane daga gidajensu.

https://p.dw.com/p/4ZS40
Mutane a cikin ambaliya a Mombasa na kasar KenyaHoto: REUTERS

Shugaba Wiliam Ruto ya ce matsalar ambaliyar ruwa babbar matalsa ce da ke bukatar mataki na gaggawa, yy ce tituna da dama musamman a arewacin kasar sun lalace, inda manyan motocin da ke dauke da abinci da magunguna da kuma man fetur suka makale.

Mr Ruto ya ce an bukaci rundunar tsaron Kenya da ta kai kayan agajin jiragen sama ga al'ummomin da bala'in ya shafa, yayin da gwamnati ta samar da shilling biliyan 2.4 kusan dalar Amirka miliyan 16 don samar da abinci ga ‘yan gudun hijirar.

Kasashen Kenya da Somaliya da ke makwabtaka da Habasha,  na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru arba'in, yanzu haka kasashen na fuskantar mummunar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama mai alaka da yanayin El Nino.

Yanzu haka dai kungiyar agaji ta Red Cross ta kaddamar da asusun neman agajin dala miliyan 20 don magance matsalar, ana ta bangaren majalisar dokokin kasar Kenya za ta yi zama a ranar Litinin don tattauna shawarwarin yadda za a shawo kan wannan matsala da ta addabi al'ummar kasar.